What is Nostr?
BBC /
npub1kw3…th47
2024-07-17 14:52:30

BBC on Nostr: Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/07/2024 ========== ...

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/07/2024
==========

Gwamnonin PDP sun isa Enugu domin taron su na ƙasa. Sarki Charles ya gabatar da tsare-tsaren sabuwar gwamnatin Birtaniya. An sako mahaifiyar Rarara bayan mako uku da sace ta. An kashe ƙarin mutum huɗu yayin zanga-zangar adawa da gwamnati a Kenya. IMF ta rage hasashen bunƙasar tattalin arzikin Najeriya. Sudan ta yi watsi da buƙatar jibge sojin Iran a gaɓar tekun Maliya. Ƙungiyar IS ta ɗauki nauyin kai harin masallacin Oman. Biden zai yi sauye-sauye a kotun ƙolin Amurka. Turkiyya da Nijar suna tattaunawar ƙulla ƙawancen soji da tattalin arziki. Gwamnan Kano ya naɗa sabbin sarakuna uku masu daraja ta biyu. Medecins sans Frontieres ta roƙi ƙungiyoyin agaji su koma ayyukan su a Sudan. Trump ya samu goyon bayan tsofaffin abokan hamayyarsa.

#Nigeria #Pdp #Uk #Kenya #Imf #Sudan #Oman #Usa #Turkey #Kano

https://www.bbc.com/hausa/live/c19k0dyzm2wt
Author Public Key
npub1kw3qwhz0z5sazlhkedhgdy0yxp7pknp45cz4n0ytzfnkytmd8r6qltth47